Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya bayyana yadda jamiāan tsaro suka hana shi tarbar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.
Ortom ya shaida yadda ya je har filin jirgin sama na rundunar sojin saman Najeriya da ke Makurdi a ranar Asabar duk domin ya tarbi Osinbajo, amma aka hana shi.
Ya ce,”Duk domin nuna girmamawa na saki duk ayyukan na a jihar, na nufi filin jirgin wanda na yi danasanin zuwa, saboda an tozarta ni
The Nation ta rawaito cewa, Osibanjo ya zarce Wukari a Jihar Taraba, bayan saukar ta sa daga jirgin sama.