Kalaman fitaccen mawakin siyasar nan a Najeriya, Dauda Kahutu Rarara na ci gaba da tayar da kura a cikin ƙasar bayan da ya fito ya soki irin salon mulkin da tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya yi.
Wani bidiyon mawakin da ya karaɗe shafukan sada zumunta, ya nuno shi yana cewa sai da “Buhari ya kashe ƙasar kafin miƙa ga shugaba Tinubu.”
Ya ce ya yi da-nasanin gudummawa da ya bai wa tsohon shugaban ƙasar.
“Na yi da-na-sani saboda kyakkawan zaton da na yi wa Buhari na kawo gyara a Najeriya. Amma ba mu ga haka ba har ya gama mulki,” in ji Rarara.
Ya ce Buhari ya kashe kowanne fanni a ƙasar kafin ya miƙa mulki ga gwamnatin da ke kai a yanzu.
“Duk wata ma’aikata ko hukuma gwamnatin Buhari ta kasheta, sai an motsa ta take motsi,” a cewar mawakin.
Ya kuma ce kwana 100 na gwamnatin Tinubu, ta fi ta shekara takwas ɗin mulkin Buhari.
Dangane da batun naɗa ministoci a gwmanatin Tinubu kuwa, Rarara ya ce kafin naɗa su ya kamata a nemi shawararsa.
“Idan har ba a ba ni muƙamin minista ba, to ya kamata a ce an kira ni an zauna da ni, sannan an zaɓi waɗanda za a bai wa mukaman ministoci da ni,” in ji Rarara.
“Ni na wuce a ba ni muƙami ɗaya sai dai muƙamai. Ni ba wanda za a yi gefe da ni ba ne, dole a dama da ni,” in ji shi.
Sai dai kalaman na Rarara sun haifar da martani daga angarori da dama.
Tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kan kafafen yaɗa labaru na zamani, Malam Bashir Ahmad, ya kwatanta kalaman mawakin a matsayin “marasa kan-gado”.
“Maganganunsa sun saɓa hankali da tunani. Babu hikima a cikinsu ko kaɗan.”
Game da wakokin da ya yi wa Buhari, Bashir ya ce Rarara bai taɓa yi wa tsohon shugaban ƙasar waka kyauta ba, ba tare da an biya shi hakkinsa ba.
Dauda Kahutu ɗaya ne daga cikin mawaƙan arewacin Najeriya waɗanda suka yi fice a harkar siyasa.
Kuma a cikin shekarun nan ya kan alaƙanta kansa da jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar.
Ya rera waƙoƙi na goyon bayan tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari waɗanda suka yi tashe, sannan ya rera wa shugaban ƙasar mai ci, Bola Ahmed Tinubu waƙoƙi na nuna goyon baya tun lokacin yaƙin neman zaɓe da kuma bayan samun nasara.