Shugaban Liberia, George Weah, ya amince da shan kaye a zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu da aka gudanar a makon da ya gabata.
Mista Weah ya shaida wa ‘yan ƙasar a wani jawabi da ya gabatar a kafar rediyon ƙasar cewa jam’iyyarsa ta fadi zaɓe, sai dai kuma Liberia ta yi nasara.
Bayan kammala ƙidaya kusan dukkanin ƙuri’un da aka kaɗa, jagoran ‘yan adawa Joseph Boakai ke kan gaba da ‘yar tazara kaɗan na kashi 51 cikin 100.
Zarge-zarge rashawa na daga cikin batutuwan da suka dabaibaye Mulkin shugaba Weah, amma kuma amincewa da shan kaye ya kafa tarihi a karo na biyu na miƙa mulkin dimokuradiya a cikin shekaru shida.
Kuma wannan shi ne zaɓe na farko tun bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta kawo ƙarshen ayyukanta na wanzar da zaman lafiya shekara biyar da suka gabata sakamakon yaƙin basasa a ƙasar.