fidelitybank

Na yanke ‘ya’yan Marainana saboda na nesanta da mata – Bob Korna

Date:

Wani mutum a jihar Binuwe mai suna Terhemen Anongo ya yanke ’ya’yan marainansa biyu, domin gudun duniya da kuma kauce wa fadawa halaka.

Terhemen Anongo mai shekaru 44, wanda aka fi sani da ‘Doc K’ ko ‘Bob Korna’ a yankin Gboko na Jihar Binuwe, ya ce, a yanzu rayuwa ta fi masa dadi bayan wannan hukunci da ya yanke.

A wata hira da ya yi da Aminiya a Makurdi, babban birnin Jihar Binuwe, Anongo ya ce, ba haka siddan ya yanke ’ya’yan marainansa ba, sai dai ya yi hakan ne domin ya yi nesa-nesa da sha’awar ’ya’ya mata wanda hakan zai ba shi damar tsantsanta bauta ga Ubangijinsa ba tare da wani abu ya dauke masa hankali ba.

Tun a watan Maris na bara ne labarin Anongo ya bulla, a lokacin da ya yanke daya daga ’ya’yan marainansa da kansa wanda a sanadiyar haka ya kusa rasa ransa.

Sai dai bayanai sun ce, da yake yana da kwanaki a gaba, wasu kwararrun likitoci da suka yi masa rubdugu wajen fahimtar halin bukata da yake ciki suka ceto ransa ta hanyar yi masa tiyata bayan ya yi asarar jini mai tarin yawa.

A ranar Litinin ta makon da ya gabata ce, Anongo ya yanke dan marainansa na biyun, inda ya sake nanata cewa, hakan zai ba shi damar tsantsanta bauta ga Ubangijinsa ba tare da mata sun dauke masa hankali ba.

Tarihi dai ya nuna cewa, tun a aji na biyar Anongo ya yi watsi da karatun likitanci da yake yi a Jami’ar Ibadan, inda ya koma mai tura baro a yankin na Gboko.

“Na shiga Jami’ar Ibadan a shekarar 1996, kuma a shekarar 2000 har na ci jarrabawar da za mu tafi Asibitin Koyarwa na Jamiar domin karbar horo a kan makamar aiki, sai na yanke shawarar watsi da karatun saboda matsananciyar damuwa da nake fama da ita.

“A lokacin na daina sha’awar karatun gaba daya, sai dai kuma daga baya na yi kokarin komawa karatun amma mahukuntan jami’ar suka ce da ni ai ta faru ta kare.

“Na yanke dan marainan nawa na farko a ranar 10 ga watan Janairun 2021, sai dai an samu tangarda domin kuwa kwayoyin cututtuka sun shiga jikina, amma hakan bai hana na ci gaba da gudanar da harkokina ba har zuwa lokacin da na warke kuma yanzu garau nake don babu abin da ke damu na.

“A wancan lokaci ina aiki ne a wani Kamfanin Sufuri da ake kira Flight, amma sai suka sauya tsare-tsarensu na gudanarwa, wanda hakan ya sanya na ajiye musu aikinsu.

“A halin yanzu ina rayuwa ta cikin annashuwa da jin dadi kasancewar ina abokai masu kirki da suka rika kula da ni, akwai yan uwana mata da suka rika aiko min da abun alheri lokaci bayan lokaci.

“Na ajiye kayan abinci da dama a gidana, kuma duk lokacin da nake da wata bukata na kan tashi na girka da kaina. Na kuma rika biyan mutanen da suka kula da ni asibiti. A cewar Bob Korna.

hausa news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp