Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya ce ya yafe wa Shugaba Muhammadu Buhari.
Ortom ya bayyana haka ne a yayin wata hira da ake yi da shi a shirin safiya na The Morning Show na tashar talabijin ta Arise a yau Laraba.
Gwamnan ya kasance yana sukar fadar shugaban kasar a kan yadda ya ce gwamnatin tarayyar na sukar gwamnatinsa a kan kashe-kashen da ake yi a jiharsa.
A baya-bayan nan shugaban kasar ya nemi afuwa daga ‘yan kasar da suke ganin mulkinsa ya kuntata musu.
Sai dai kuma ya shawarci shugaban mai barin-gado da ya tsaya a kasar ya taimaka wa sabuwar gwamnati mai zuwa ta Bola Tinubu, domin ciyar da kasar da ma jiharsa gaba, kamar yadda ya ce.