Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya ce shi ne mutumin da aka fi ”ɓata wa suna” a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan.
Yayin da yake jawabi a lokacin ƙaddamar a littafin tsohon ministan shari’ar ƙasar, Mohammed Bello Adoke da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, Shettima ya ce Jonathan ya taɓa kawo shawarar cire shi daga muƙaminsa na gwamnan jihar Borno.
Amma sai tsohon ministan ƙasar, kuma babban lauyan gwamnati, Mohammed Bello Adoke ya ba shi shawarar kauce wa yin hakan.
Shettima ya ce Adoke ya nuna jarumta wajen faɗa wa Jonathan cewa kundin tsarin mulki bai ba shi damar cire ko da zaɓaɓɓen kansila, balle gwamna sukutum.
Kawo yanzu dai tsohon shugaban ƙasar, GoodLuck Jonathan bai mayar da martani dangane da iƙirarin na Kashim Shettima ba.
A watan Mayun 2013 ne Jonathan ya ayyana dokar ta ɓaci kan jihohin da ke fama da rikicn Boko Haram da suka haɗa da Borno da Yobe da kuma Adamawa, to amma bai dakatar da gwamnonin ba.
Kashim Shettima ne gwamnan jihar Borno har tsawon wa’adi biyu, daga 2011 zuwa 2019, kuma ya mulki jihar a daidai lokacin da rikicin Boko Haram ya munana a yankunan arewa maso gabashin Najeriya.