Tsohon Shugaban ƙasa,Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa, ɗaya daga cikin kurakuran da ya tafka a rayuwarsa shi ne zaɓar mataimaki a 1999.
Obasanjon ya bayyana haka ne a yayin da yake amsa tambayoyi a wani taro na wasu ɗalibai a Abeokuta da ke Jihar Ogun.
Obasanjo dai shi ne ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa a shekarun 1999 da 2003, inda Atiku Abubakar ya zama mataimakinsa.
“Ba zan ce bana kuskure ba – Na yi su da yawa,” in j iObasanjo.
“Amma wani abu da ya faru da ni shi ne Ubangiji bai taɓa kunyata ni ba. Kuma wannan abu ne mai muhimmanci.
“Misali, ɗaya daga cikin kurakuran da na yi shi ne ɗaukar mataimaki lokacin da zan zama shugaban ƙasa.
“Sakamakon wannan kuskure ne mai kyau, Ubangiji ya kare ni,” in ji Obasanjo.