Wani magidanci mai shekaru 43, Yusuf Hassan, ya shaidawa ‘yan sanda a jihar Ogun dalilin da ya sa ya yanke shawarar cinnawa gidan tsohouwar masoyiyarsa wuta domin ya kone ta har lahira.
Hassan ya ce, tsohon masoyar tasa, Busayo Falola, ta ki amincewa da duk wani yunkuri na sasanta su, inda ya ce yana jin abu na gaba shi ne ya kona dakinta.
Karanta Wannan: An ƙone motar hukumar kiyaye haɗura ƙurmus a Bauchi
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, an kama Hassan ne a ranar 4 ga watan Afrilu bayan da ya kona ginin baki daya.
Kamen wanda ake zargin, Oyeyemi ya ce, ya biyo bayan rahoton da mai gidan da abin ya shafa, wata mata ‘yar shekara 62 mai suna Adejoke Salau ta kai hedikwatar ‘yan sanda ta Ago Iwoye.