Ɗanwasan gaban ƙungiyar Barcelona ta Spain, Robert Lewandowski ya ce a shekarun baya saura ƙiris ya koma ƙungiyar Manchester United ta Ingila.
“Manchester United ta nemi ni, har na amince. A lokacin ina a burin komawa ƙungiyar ne domin aiki da fitaccen koci, Alex Ferguson.”
Lewandowski ya ce lamarin ya faru ne a shekarar 2012, a lokacin da yake ganiyarsa sosai a ƙungiyar Borussia Dortmund ta Jamus.
A cewarsa, “Dortmund ce ta hana ni komawa saboda a lokacin ba su shirya rabuwa da ni. Sun yi tunanin idan na ƙara tsayawa, zan ƙara daraja kuma za su samu ƙarin kuɗi. Amma lallai ni a lokacin har na amince da tayin Man United,” in ji shi.