Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa a shirye yake ya jagoranci gamayyar jam’iyyun adawa don kawar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a 2027.
Atiku ya bayyana hakan ne a sakon taya murna ga gwamnonin jam’iyyar PDP, wadanda kotun koli ta amince da zabensu a ranar Juma’a.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun ofishin yada labarai a Abuja, Atiku ya bayyana hukuncin kotun a matsayin albishir ga al’ummar jihohin Bauchi da Filato da Kuros Riba da kuma Zamfara, kuma hakika nasara ce ga tsarin mulkin dimokradiyya.
Ya kuma jaddada matsayinsa na cewa hadin kan ‘yan adawa ne kadai zai iya karfafa dimokradiyya a Najeriya.
An jiyo Atiku yana cewa, “Ni a shirye nake kamar yadda aka saba, domin in jagoranci wannan mukami, tare da dukkan shugabanninmu da Gwamnoninmu, domin ci gaban kasarmu.”
A cewarsa, “Inda aka ga an yi adalci sosai, mu a matsayinmu na masu kishin kasa da kuma ‘yan kasa, za mu yaba.”
Hakazalika Atiku ya ce bisa hukuncin kotun koli, “akwai tabbacin ci gaba da tsare-tsaren shugabanci nagari da PDP ta kawo a jihohinsu.”
Ya yi kira ga gwamnonin PDP, wato: Bala Mohammed na Bauchi, Dauda Lawal na Zamfara, Barr. Caleb Muftwang na Filato da Fasto Umo Eno na Akwa Ibom don ganin nasarar da suka samu a kotun koli a matsayin wata dama ce ta karfafa tare da fadada fa’idar shugabanci nagari da suka riga suka kafa.