Donald Trump ya shaidawa dubban magoya bayansa a wani gangamin yakin neman zaben jam’iyyar Republican a jihar Michigan cewa, yana da tabbacin zai lashe zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamba.
Ya musanta cewa yana barazana ga dimokuradiyya, yana mai cewa garin kare dimukradiyyar ne ma ya kusa rasa ransa.
Mista Trump ya yi ta yi wa Joe Biden shaguɓe, yana mai cewa har yanzu jam’iyyar Democrat ba ta san wanda zai zama dan takararta a watan Nuwamba ba.
Ya kuma sake nanata ikirarin cewa, idan aka zabe shi, zai gudanar da abin da ya kira korar bakin haure mafi girma a tarihin Amurka.
Jihohi a tsakiyar yammacin kasar ciki har da Michigan ne ake sa ran za a kai ruwa rana a kansu a zaben na Nuwamba mai zuwa. In ji BBC.