Dan wasan Bayer Leverkusen, Victor Boniface, ya dage da cewa zai tabuka abun arziki a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da Najeriya za ta yi da Lesotho a 2026.
Ana sa ran Boniface zai taka rawar gani a Super Eagles idan babu Victor Osimhen.
Dan wasan mai shekaru 22 ya taka rawar gani a kulob din Bundesliga, Bayer Leverkusen a kakar wasa ta bana.
Dan wasan ya zura kwallaye bakwai kuma ya taimaka biyar a wasanni 11 da ya buga wa Die Werkself a kakar wasa ta bana.
Boniface ya kuduri aniyar yin kwafin tsarin kulob dinsa a fagen kasa da kasa.
“Na shirya kuma na mai da hankali; mun kuduri aniyar, don haka za mu ga abin da zai faru,” in ji shi a NFF TV bayan atisayen karshe da kungiyar ta yi a ranar Laraba.
“ Horon ya yi kyau sosai; mun yi horo biyu cikin kankanin lokaci kuma kowane dan wasa ya mai da hankali kan wasan.
“Zan yi ƙoƙari na yi iya ƙoƙarina, in ba da kashi 100 kuma in yi ƙoƙarin yin nasara a wasan. Ba za mu jira ganin magoya bayanmu a filin wasa ba saboda muna bukatar goyon bayansu.”