Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai, ya ce, shi ne ya sanar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari game da barazanar da masu jihadi suka yi cewa za su shugabanci da shi gwamnan.
Gwamman ya bayyana hakan ne a yayin wata irin da ‘yan jarida da ake yada wa kai tsaye, jiya Laraba da daddare.
Idan dai ba a manta ba karshen makon da ya gabata ne masu shigo da fitar da wani bidiyo da ke nuna mutanen da suka sace na jirgin kasa Abuja zuwa Kaduna, tun a watan Maris inda ciki ciki barazanar cewa sun kamo shugaban kasar da fito.
El-Rufai ya ce shi Buhari bai ma san da wannan barazana ba sai da ya gaya masa, sannan kuma Gwamman Jihar Zamfara Bello Matawalle ya ka iwa shugaban hoton bidiyon ya gani.
Gwaman na jihar kaduna ya ce daman shi tun a baya an gargade shi da ya yi hankali shi da bugunsa a kan wannan barazana.
Ya ce, ‘’Ta yaya za mu zama kasar da take da sojoji da ‘yan-sanda da ƙungiyoyi amma kuma ‘yan ta’adda su rika barazanar za su sace shugaban kasa?’’
Gwamnan ya ce, ai shi daman tun baya da shekara biyar yake bayar da shawarar da a shiga dajin a yi wa sansanoninsu ruwan bama-bamai, da cewa hakan ne za a yi maganinsu.
Ya ce ya gana da Shugaba Buhari ne ranar Lahadi inda ya gaya masa yadda girman wannan matsala ta tsaro yake.
Ya yi bayani da cewa, idan a baya wadanda ke cikin gwamnati suna daukar wannan abu da wasa, suna ganin abin na faruwa ne kawai a Katsina da Zamfara da Kaduna da Naija, to yanzu abin ya zo har gida, saboda haka dole ne a tashi a ga bayan mutanen.