Kyaftin din Al-Nassr, Cristiano Ronaldo, ya ce zai so ya mallaki kungiyar kwallon kafa a nan gaba.
Ronaldo ya kuma ce ya san Karim Benzema zai bar Real Madrid zuwa gasar kasar Saudiyya, ya kara da cewa wasu ‘yan wasa da dama na zuwa gabas ta tsakiya.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da alamar ruwa mai suna ‘Ursu’, an tambayi Ronaldo game da shirinsa na gaba kuma tsohon dan wasan Manchester United ya ce, (kamar yadda CristianoXtra ya fada).
“A nan gaba, zan so in mallaki kulob, ban yanke hukuncin ba.”
Da aka tambaye shi game da gasar ta Saudiyya, dan wasan na Portugal ya kara da cewa: “Na san cewa Benzema zai zo Saudiyya, kuma shi ya sa na ce gasar Saudiyya za ta kasance cikin manyan 5 a nan gaba, ‘yan wasa da yawa za su zo.”