Shugaba Bola Tinubu, ya roki matasan Najeriya da su kasance masu hakuri da fahimtar irin wahalhalun da kudurorin da gwamnatin sa ke yi na tattalin arziki.
Tinubu ya bayyana cewa, wahalhalun da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu za su gushe daga karshe kuma su ba da damar samun daidaito da wadata da tattalin arziki mai dunkulewa.
Ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Alhamis a babban birnin kasar nan a wajen wani taro da shugabannin matasan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa daga jihohi 36 na tarayya da babban birnin tarayya Abuja.
Shugaban ya ce, “Na yi wa kasar alkawari cewa, babu wata shawara da za ta yi wa wannan gwamnati wuya ta dauka, domin ci gaba da hadin kan kasar nan. Gyaran tattalin arziki na iya zama a hankali. Yi haƙuri kaɗan.
“Zan iya tabbatar muku cewa na fahimci radadin da kuke ciki. Ba shi da sauƙi a fitar da dodo sama da shekaru arba’in da ake kira tallafin mai.
Kayayyakin abinci da kayayyaki da ayyuka da suka hada da sufuri duk sun tashi sakamakon cire tallafin man fetur.


