Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya ce, ya koyi darasi daga magabatansa kamar David Mark da Bukola Saraki.
Ya kuma ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu a kan kudirorin doka fiye da kowane shugaban kasa tun 1999.
Lawan ya bayyana haka ne a daren ranar Asabar da ta gabata a cikin godiyarsa bayan samun lambar yabo ta ‘The Sun Political Icon of the Year 2021’ a bikin karramawar shekara ta 19 da jaridar ta yi a Legas.
Wannan na zuwa ne a wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman ya fitar ranar Lahadi, Ola Awoniyi, mai taken, ‘Me ya sa Majalisar Dokoki ta 9 ta yi fice daga Majalisun da suka gabata.
Lawan ya ce, “Bari in ce na koyi abubuwa da dama daga wajen wani fitaccen shugaba, kuma sunansa Sanata David Mark. Ya kasance Shugaban Majalisar Dattawa na wa’adi biyu, Majalisa ta 6 da ta 7. Kuma ba shakka, Shugaban Majalisar Dattawa na 13, yayana, kuma abokina, Sanata Bukola Saraki, wanda ya zo a wannan taron. Na yi aiki da shi a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa. Ya kuma bayar da gudunmawa kamar yadda tsohon shugaban majalisar dattawa ya yi.”