Shahararren tsohon dan wasan kasar Italiya, Fabio Cannavaro, ya bayyana cewa ya ki amincewa da tayin kocin Super Eagles ta Najeriya.
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta sanar a watan Yuni cewa za ta nada wani dan kasar waje da zai jagoranci Super Eagles sakamakon rashin nasarar da kungiyar ta yi a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA na 2026.
Cannavaro ya tabbatar da cewa hukumar NFF ta tuntube shi domin ya yi wa Super Eagles din wasa.
Tsohon dan wasan bayan Juventus da Real Madrid ya ce yana sha’awar yin aiki a Turai a yanzu.
“Na samu tayi daga Najeriya [tawagar kasa] da kungiyoyin Iran, amma ina so in jira kungiyoyin Seria A da Turai har zuwa Disamba. Bayan haka, zan iya sake fara tafiya,” La Gazzetta dello Sport.
Augustine Eguavoen ne zai jagoranci Super Eagles a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Afrika na 2025 da za su yi da Jamhuriyar Benin da Rwanda.