Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya c,e babu wanda zai iya bata masa suna kuma ba shi da gida a kasar waje a lokacin da yake mulki.
A cewar mai baiw shugaban kasa shawara na musamman a harkokin yada labarai, Femi Adesina, shugaban kasa ya bayyana haka ne a wajen taron liyafar da aka gudanar a daren jiya Litinin, wanda aka shirya domin karrama shi a Damaturu, jihar Yobe.
Ya bayyana cewa, ya na fuskantar kalubale, domin yakar cin hanci da rashawa a Najeriya.
“To, a karkashin gwamnatinsa, yaki da cin hanci da rashawa ba abu ne mai sauki ba. Ya ce, an samu sauki lokacin da ya rike mukamin shugaban kasa,” in ji Adesina.
A cewarsa, a yankin Arewa maso Gabas, da taimakon Allah, an fatattaki ‘yan Boko Haram.
“A Arewa maso Gabas, Allah ya taimake mu wajen kawar da Boko Haram, tattalin arziki ya tashi, wasu kuma suna tambayata game da nasarorin da na dauka na yaki da cin hanci da rashawa,” inji shi.