A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana bakin cikinsa kan hatsarin kwale-kwalen da ya afku a jihar Kwara, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama.
Rahotanni sun bayyana cewa, hadarin kwale-kwalen ya yi sanadiyar mutuwar mutane 103 wadanda suka halarci daurin aure a kauyen Egbu da ke karamar hukumar Patigi a ranar Litinin din da ta gabata.
Da yake mayar da martani kan wannan labari mai ban tausayi, Tinubu, a wata sanarwa da Daraktan yada labarai na fadar gwamnatin jihar Abiodun Oladunjoye ya fitar, ya ce, “Na yi matukar bakin ciki da labarin hatsarin jirgin ruwa da ya ci rayukan al’ummarmu a jihar Kwara.
“Cewa wadanda abin ya rutsa da su baki ne a wajen bikin aure ya sa hatsarin ya kara zafi.
“Tausayina da ta’aziyyata ga iyalai da abokanan wadanda abin ya shafa. Ina kuma jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Kwara bisa afkuwar hatsarin. Bari duk ƙaunatattuna su sami ta’aziyya.”
Yayin da yake kira ga gwamnatin jihar Kwara da hukumomin gwamnatin tarayya da abin ya shafa da su duba halin da ake ciki a hatsarin jirgin ruwa, shugaba Tinubu ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta duba kalubalen da ke tattare da safarar ruwa a cikin kasar nan domin tabbatar da an bi ka’idojin tsaro da aiki sosai.
“Ya kamata gwamnatin jihar Kwara da hukumomin tarayya da abin ya shafa su hada kai domin bankado musabbabin faruwar wannan hatsarin da ba a taba gani ba. Ya kamata kuma a ba da agaji cikin gaggawa da taimakon da ya dace ga wadanda suka tsira da iyalan wadanda abin ya shafa,” in ji Shugaban.


