fidelitybank

Na jikin Tinubu ne suke ɗaukar nauyin zanga-zangar nan – Gwamnan Imo

Date:

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya ce, wasu dake jikin shugaban kasa Bola Tinubu wanda ake kira Kabal da ke cin gajiyar arzikin kasar nan ke ɗaukar nauyin zanga-zangar matasa.

Uzodinma ya ce ‘yan jam’iyyar su ne suka dauki nauyin zanga-zangar da ake yi a fadin kasar nan na nuna adawa da Tinubu duk da cin gajiyar arzikin Najeriya.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, gwamnan ya kuma yabawa al’ummar yankin Kudu maso Gabas da rashin shiga zanga-zangar da aka yi a fadin kasar.

Da yake lura da cewa zanga-zangar lumana hakki ne na ‘yan kasa, Uzodinma ya jaddada cewa Tinubu ya nuna jajircewarsa wajen tunkarar kalubalen da kasar ke fuskanta.

A cewar gwamnan: “Ina yaba wa al’ummarmu na yankin Kudu maso Gabas da suka yi biyayya ga kiran da muka yi na kada su shiga zanga-zangar da ake yi a fadin kasar nan. Hikimar ku na sanin haɗarin da masu satar mutane ke yi wa masu zanga-zangar lumana abin a yaba ne da gaske.

“Yayin da zanga-zangar lumana ba shakka hakki ne na mutane, shawarar da kuka yanke na ba da fifiko ga aminci da kwanciyar hankali yana nuna taka tsantsan.

“Abin takaici ne cewa wadanda suka bayar da gudunmawa wajen kalubalen tattalin arzikin da muke fama da su a halin yanzu su ne ke daukar nauyin zanga-zangar maimakon yin aiki da FG don warware matsalar.

“Wannan martanin ya zo ne kawai saboda muna da Shugaban kasa wanda ke da karfin gwiwa don wargaza baragurbin da ke cin gajiyar albarkatunmu.”

legit.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp