Bayan yanke hukuncin da kotu ta yankewa wanda ya kashe Hanifa Abubakar mai shekaru biyar Tanko Abdulmalik da wanda ake zargi Hashimu Ishyaku hukuncin kisa ta hanyar rataya, Abubakar Abdulsalam, mahaifin marigayin ya bayyana farin cikinsa da cewa, Hanifa ta samu adalci daga kotu.
Abdulsalam, a lokacin da yake zantawa da jaridar The Punch ya yabawa kotun bisa hukuncin da ta yanke.
Ya ce, “Na ji dadin yadda Hanifa ‘yata ta samu adalci.
“Mun yaba da kokarin kowa da kowa, a cikin wannan yanayin, an yi adalci da kyau,”
“A gaskiya na yi takaitattun kalmomi don nuna godiyata da godiya ga al’ummar Kano. Muna matukar godiya da su domin sun tsaya mana a lokacin gwaji kuma ba za mu taba mantawa da wannan karramawa guda daya ba.
Ya kara da cewa “Allah ya riga ya yanke hukuncin tun kafin zuwan kotun, kuma ina godiya ga kotun da ta yanke hukunci.”
Ku tuna cewa an sace marigayiya Hanifa a wani lokaci a cikin Disamba 2021, ta hannun mai gidanta, Tanko.