Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce, ya ji daɗi kan yadda Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya ke nemansa don kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa.
Tinubu ya yi masa tayin muƙami a gwamnatin, sai dai Kwankwaso ya ce har yanzu ba su kai ga cimma matsaya ba.
Sanata Kwankwaso ya bayyana haka ne lokacin da yake yi wa BBC ƙarin bayani kan ganawar da suka yi da shugaban kasar a ranar Juma’a ta kimanin sa’a biyu.
Tattaunawar na zuwa ne a daidai lokacin da dambarwa ke ƙara kamari tsakanin ɓangaren sabuwar gwamnatin Kano da kuma gwamnatin APC da ta shuɗe.