fidelitybank

Na hango tashin Bam a gasar cin kofin AFCON – Malamain Majami’a

Date:

Wani malamin majami’a, Nigel Gaisie  ya yi gargadi game da harin ta’addanci a lokacin gasar cin kofin nahiyar Afirka, AFCON, da za a fata a Kamaru.

Gaisie ya bayyana cewa ya hango ‘yan ta’adda sun tayar da bama-bamai a wani filin wasa a lokacin gudanar da gasar AFCON.

Da ya ke jawabi ga mambobinsa, malamain dan kasar Ghana ya bukaci kasashen da ke halartar gasar da su yi addu’a, domin kaucewa bala’i a lokacin gasar da za a yi a kasar Kamaru.

A cewar Gaisie: “Wannan annabci ne na duniya. Ubangiji ya dauki ruhina zuwa wuri kamar Kamaru game da gasar cin kofin Afirka na 2021.

“Na ga wani abu kamar ‘yan wasa a tsaye a kan gado kuma suna jin zafi yayin da wasu daga cikinsu ke kuka.

“Bari al’ummar Kamaru su yi addu’a da duk wata tawagar da ta cancanta su yi haka, domin ina ganin wani abu kamar harin ta’addanci da hare-haren bama-bamai.

“Ina ganin cewa wani abu ya faru a filin wasa kuma duk wurin ya kasance cikin rikici kuma mutane sun mutu.” Inji Gaise.

DAILY POST ta rawaito cewa,  gwamnatin Ghana ta gargadi fastoci game da fitar da annabce-annabce da za su haifar da firgici da fargaba.

A ranar Lahadi 9 ga watan Janairu, 2022 za a fara gasar AFCON ta shekarar 2021 a kasar Kamaru.

A halin da a ke ciki dai kungiyar Super Eagles ta Najeriya ta isa kasar Kamaru gabanin fara gasar.

 

bbc news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Isra’ila na zargin Canada da goyon bayan Hamas – Netanyahu

Isra'ila ta zargi Canada da taimaka wa Hamas bayan...

Rashin tallafin agaji ka iya dawo da Boko Haram a Najeriya – MDD

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta...

Yin gini a kan hanyoyin ruwa ne ya janyo ambaliyar Maiduguri – NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa da Najeriya NEMA ta...

Amnesty ta yi Allah wadai da tsare Sultan kan bidiyon lafiyar Tinubu

Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta yi...

Dalilin da ya sa na gana da Tinubu – Kofa

Ɗan majalisar tarayyar mai wakilitar Kiru da Bebeji daga...

Ba za mu jingine yajin aiki ba har sai an biya mana buƙatun mu – Ma’aikatan Jinya

Shugaban ƙungiyar ma'aikatan jinya ta Najeriya, Morakinyo-Olajide Rilwan ya...

Za a fara yi wa Dalibai gwajin kwaya kafin su shiga jami’a – NDLEA

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta fara yi wa...

Za mu kammala titin jirgi na Kaduna zuwa Kano a 2026 – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya, ta ce za a kammala aikin titin...

Adadin kudaden da Liverpool ta kashe wajen daukar ‘yan wasa

Liverpool ta kashe fam miliyan 265 wajen ɗauko ƴanƙwallon...

Sunderland ta ɗauko ƴanƙwallo bakwai a kakar bana

Granit Xhaka ya zaman ɗan ƙwallo na bakwai da...

James Trafford ya sake komawa Man City daga Burnley

Mai tsaron ragar tawagar Ingila, mai shekara 21, James...

Luiz Diaz ya kammala komawa Bayern Munich daga Liverpool

Luis Diaz ya kammala komawa Bayern Munich daga Liverpool...
X whatsapp