Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ya bayyana jin dadinsa kan yadda ake gudanar da jarrabawar gama-gari ta shekarar 2023 ta UTME.
Kakakin hukumar ta JAMB, Fabian Benjamin ya bayyana cewa akalla dalibai 80,000 da suka kasa zana jarabawar UTME ta 2023, sun sake zana jarabawar a Najeriya.
Adamu ya ce ya gamsu da yadda ake gudanar da jarrabawar cikin sauki.
Ya yi wannan jawabi ne tare da magatakardar hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, Ishaq Oloyede, a lokacin da suka ziyarci cibiyar jarabawar Computer da ke unguwar Mambila Barrack a unguwar Asokoro a Abuja.
A cewar Adamu: “Na yi matukar farin ciki da abin da na gani. Dakin (na wucin gadi) (na ’yan takara), da kuma tsarin da za su yi jarabawar, ina ganin komai ya daidaita.”
Adamu ya yi nuni da cewa, ba a samu wani mugun abu ba a yadda ake gudanar da jarabawar UTME a cibiyoyin CBT da aka ziyarta.
Haka kuma ya gabatar da shari’ar wani wuri na wucin gadi ga ‘yan takarar da ke jiran lokacin da aka tsara za su yi jarrabawar.
Ya yi nuni da cewa samar da ajujuwa wani cigaba ne da ake bukata.