Aminu Waziri Tambuwal ya bukaci jam’iyyar PDP da ta tattara ayyukanta, ta kuma matsa kaimi wajen ganin ta fito da dan takarar shugaban kasa da ‘yan Najeriya za su kasance a shirye su mara masa baya a zaben 2023.
Dan takarar shugaban kasar dai, ya ce yana da dukkan abubuwan da ake bukata, domin cika sharuddan da ‘yan Najeriya ke nema.
Tambuwal ya bayyana haka ne a yammacin Larabar da ta gabata a lokacin da ya gana da taron tsaffin ministocin tarayyar Najeriya karkashin jam’iyyar PDP a Asokoro, Abuja.
“Abin da ke da mahimmanci ga PDP shi ne dan takara da za mu iya yin aiki tare, don kai mu ga ci wannan zabe, ba daga inda mutum ya fito ba,” Gwamnan Sokoto ya shaida wa tsoffin shugabannin kasar.
Da yake bayyana cewa, son kai da kishin kasa da hadin kan al’ummar kasar ne ke neman sa na neman babban mukami a kasar, ya ce “ba wani abu ba ne na kashin kai. Ya shafi kasarmu gaba daya.”
Da yake magana shaidarsa na uku wanda ya rataya a kan bangaren zartarwa, majalisa, da shari’a, ya jaddada cewa yana da kyakkyawar fahimtar kasar, inda, abin takaici, “abubuwa suna kara tabarbarewa.”