Gwamna Sani Bello na jihar Neja ya ce, ya dauki tsawon lokaci ya na rike da mukamin mukaddashin shugaban APC na kasa.
Bello ya bayyana hakan ne a sakatariyar jam’iyyar mai mulki da ke Abuja bayan ya jagoranci wani taron kwamitin riko.
Ya ce, tun bayan da Gwamna Mai Mala Buni ya yi tafiya, shi ne ke jan ragamar iko na jam’iyyar.