Gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade, ya bayar da wa’adin sa’o’i 24 ga duk masu rike da mukaman siyasa da ke da sha’awar tsayawa takarar mukaman siyasa da su yi murabus ko kuma kafin karfe 12 na rana ranar Alhamis.
A wata sanarwa dauke da sa hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Christian Ita, Ayade ya bayyana cewa, duk wani dan siyasa da ke rike da mukamin gwamnati, amma yana son neman mukami yana da ‘yancin yin hakan, amma sai ya mika takardar murabus dinsa ko kuma kafin karfe 12 na rana 5 ga Mayu 2022.
Gwamna Ben Ayade ya ba da umarnin cewa, duk wani dan siyasa da ke rike da mukamin gwamnati a halin yanzu amma yana son neman mukami a zaben 2023 mai zuwa yana da ‘yancin yin hakan.