Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya amince da wa’adin watanni uku ga masu filayen da ba a gina su ba 189 a yankin domin su fara raya su ko kuma a soke musu takardar rabon su.
Daraktan yada labarai da sadarwa na hukumar babban birnin tarayya Abuja, Muhammad Sule, ya bayyana hakan a ranar Lahadin da ta gabata a Abuja cewa, masu mallakar mallakin sun samu amincewar tsarin ginin amma har yanzu ba su ci gaba da gina kadarorin ba.
Sule ya bayyana cewa, ana sa ran masu kadarorin da abin ya shafa za su bunkasa kadarorin a cikin wa’adin da aka kayyade ko kuma a kwace musu takardun mallakarsu kamar yadda doka ta tanada.
Ya bayyana cewa, wa’adin ya shafi daidaikun mutane da kungiyoyi da suka nuna sha’awar bunkasa kadarorinsu ta hanyar samun amincewar tsarin gini.
Sule ya kara da cewa cibiyoyin gwamnati da ke da takardun mallakar filaye a cikin babban birnin tarayya Abuja amma har yanzu ba su ci gaba da bunkasa ba an kuma shawarce su da su yi hakan cikin wa’adin watanni uku don kaucewa takunkumi.
NAN ta ruwaito Sule yana cewa, “Ministan ya mika wannan karimcin ga masu kadarorin 189, saboda burinsu na bunkasa kadarorin ta hanyar samun amincewar tsarin gini, wani sharadi na bunkasa duk wata kadara a babban birnin tarayya Abuja.” Inji Sule.
“An cire masu filayen ne daga kwacewa saboda sun riga sun nuna kwarin gwiwa na bunkasa kadarorin su ta hanyar samun wasu takardu daga Hukumar FCT.
“Ministan yana kira ga masu mallakar kadarorin da abin ya shafa da su yi amfani da wannan damar tare da bunkasa filayensu daidai da sharuɗɗan Bayar da Haƙƙin mallaka.”