Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara, ya amince da shan kaye da ya sha a zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Gwamna mai ci ya sha kaye a hannun dan takarar gwamnan PDP, Dauda Lawal Dare.
Gwamnan a wani sakon faifan bidiyo da ya aikewa al’ummar jihar ya ce dole ne shi da dukkan magoya bayansa su mika wuya ga ikon Allah domin al’amura su na faruwa ne da yardarsa kawai, ya kuma yi fatan alheri ga zababben gwamnan yayin da yake tafiyar da al’amuran jihar.
Ya bayyana cewa gwamnatin sa a lokacin da ta fara aiki, ta gana da dukkan manyan masu ruwa da tsaki a jihar kan yadda za su iya maido da dawwamammen zaman lafiya ta hanyar tattaunawar zaman lafiya.
Sai dai ya koka da cewa har zuwa yau babu wani abu da ya fi kalubalanci kamar rashin tsaro da ke janyo asarar rayuka da lalata dukiya.
Gwamnan ya bayyana cewa baya ga tattaunawar zaman lafiya da ‘yan fashi da makami, ya yi bakin kokarinsa wajen ganin gwamnatinsa ta shigo da bangarori daban-daban na siyasa a cikin dandali daya na zaman lafiya da hadin kai a jihar domin jama’a su rika gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
Gwamnan ya ce, “Mun samu sulhu a siyasance kuma hakan ya share fagen yakin neman zabe cikin lumana da kuma harkokin siyasa masu inganci a jihar.”
cewa idan ya sani ko bai sani ba ya yi laifi ko ya cutar da wani mutum,
Matawalle ya kuma nemi gafarar duk wanda ya sani ko bai sani ba ya bata masa rai ko ya cutar da su, ya kara da cewa shi mutum ne kamar kowa kuma aikin Allah Madaukakin Sarki ne kadai ba shi da kuskure.
Ya kuma yi kira da a kwantar da hankula tare da tausaya wa wadanda suka yi hasarar dukiya da sunan biki, inda ya jaddada cewa su fahimci cewa ba su da wani wuri sai jihar Zamfara.
Ya kuma yi kira ga gwamnati mai jiran gado da ta zage damtse wajen dawo da zaman lafiya a jihar tare da nuna jin dadin gwamnatin bisa jajircewa da aiki tukuru da jajircewar al’ummar jiharsu.