Dan jam’iyyar Labour Party, Keir Starmer, ya zama sabon Firaminista bayan nasarar da ya samu a babban zaben kasar Birtaniya.
Da yake jawabi ga taron jama’a a tsakiyar London bayan nasararsa, Starmer ya ce: “Mun yi hakan, canji ya fara yanzu. Yana jin dadi, dole ne in faɗi gaskiya. ”
An ayyana jam’iyyar Labour a matsayin wadda ta lashe zaben a hukumance bayan da ta kai kujerun majalisar dokoki 326 da ake bukata.
Da yake mayar da martani kan kayen da ya sha, Firayim Minista mai barin gado, Rishi Sunak, ya ce ya dauki alhakin asarar jam’iyyar Conservative.
Sunak ya ce: “Birtaniya ta yanke hukunci mai ratsa jiki. A wannan dare mai wahala, ina so in nuna godiyata ga mutanen mazabar Richmond da Northallerton saboda ci gaba da goyon bayanku.
“Jam’iyyar Labour ta lashe wannan babban zaben kuma na kira Sir Keir Starmer don taya shi murnar nasarar da ya samu.
“A yau, mulki zai sauya hannu cikin lumana da tsari, tare da fatan alheri daga kowane bangare. Wannan abu ne da ya kamata ya ba mu gaba daya kwarin gwiwa kan zaman lafiyar kasarmu da makomarmu.
“Mutanen Biritaniya sun yanke hukunci a daren yau, akwai abubuwa da yawa da za a koya… kuma na dauki alhakin asarar.”