Shugaba Bola Tinubu ya ce, ya kuduri aniyar sauya labarin Najeriya domin amfanin ‘yan Najeriya baki daya.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Lahadi a birnin Makkah na kasar Saudiyya.
Tinubu ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar sauya labarin ta hanyar yin gyare-gyare da tsare-tsare da manufofin da za su amfana daga ‘yan kasa.
”Halin kasar har yanzu bai kai ga matakin da muke bukata ba. Yana buƙatar aiki tuƙuru da addu’o’i masu tsayi da kowane ɗayanmu. Mun himmatu wajen yin amfani da karfinmu wajen fitar da wannan damammaki domin amfanin daukacin ‘yan Nijeriya.
‘’Shi ya sa muke nan, kuma Allah Ya karba mana dukkan addu’o’inmu na daidaiku da jama’a, don amfanin kasa da al’ummarta. Akwai bukatar in godewa Allah akan abin da ya yi mini.
‘’Dole ne in yi godiya ga Allah a duk wata dama da za ta samu,’’ NAN ta ruwaito.