A ranar Laraba ne shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa Sanata Barau Jibri,n ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban majalisar dattawa a majalisar wakilai ta 10.
Barau mai wakiltar Kano ta tsakiya ya yi alkawarin fara yakin neman zabensa nan da makonni masu zuwa a hukumance.
Da yake zantawa da manema labarai a ranar Larabar da ta gabata, Sanatan ya bayyana cewa shi ne ya fi kowa kima da gogewa a cikin wadanda ke neman mukamin tare da shi.
Ya ce: “Na yi niyyar neman zama Shugaban Majalisar Dattawa ta 10. Zan ayyana kuma in fara yakin neman zabe a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa. Majalisa wani bangare ne na gwamnati wanda ba ya aiki bisa ga ra’ayi amma yana aiki akan iyawar ku don samun aikin.
“Ku tuna cewa David Mark Kirista ne, Ike Ekweremadu, Mataimakinsa Kirista ne, kuma Patricia Etteh, Shugaban Majalisar Kirista ne saboda su ne suka fi kowa daraja, gogayya kuma al’ada ce, don haka muna mayar da cancanta zuwa wasu ra’ayoyi.
“A bayyane yake a cikin dokar majalisar dattawa cewa zaben ofishin shugaban majalisar dattawa zai kasance daidai da kwarewa da matsayi. Kuma a cikin masu neman mamaye wannan ofishin, ina da matsayi mafi girma da gogewa.”