Ƙasar Kuwait ta ayyana hutun kwana 40 domin alhini da jimamin mutuwar Sarkin Kuwait Sheikh Nawaf Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah.
Ministan da ke kula da harkokin majalisar zartarwa ta ƙasar ne ya sanar da hakan, sannan kuma an rufe duk wasu wuraren aiki har na tsawon kwana uku.
A wani mataki na nuna alhini daga ƙasashen Larabawa game da mutuwar Sarkin Kuwait Sheikh Nawaf Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah, ƙasashen Masar da Lebanon da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun ayyana hutun kwana uku domin alhini.
Bayan ga hutun kwanaki ukun an kuma sassauta tutoci ƙasa a duka ofisoshin ƙasar da na jakadanci a duka ƙasashen, kuma za a fara makokin ne daga ranar Asabar.
Wannan dai gagarumin rashi ne da aka yi ga duniyar larabawa wanda kuma za a dade ana jimami.
Allah ya yi wa Sarki Kuwait Sheikh Nawaf al-Ahmad al-Jaber al-Sabah rasuwa yana da shekara 86 a duniya.
Sheik shi ya jagoranci ƙasar mai arziƙin man fetur na tsawon shekaru uku da suka gabata bayan karɓar jagorancin ƙasar daga ɗan uwansa Sheikh Sabah al-Ahmed al-Sabah.
“Cikin baƙin ciki da juyayi, muna makokin… mutuwar Sheikh Nawaf al-Ahmad al-Sabah” cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na ƙasar.
An naɗa Sheikh Nawaf a matsayin yarima mai jiran gado a 2006 kuma a 2020 ya zama sarki.
A baya ya taɓa rike muƙamin ministan tsaro da harkokin cikin gida.
Kuwait wadda ke da yawan mutane da suka kai miliyan 4.8 ciki har da ‘yan ƙasashen waje miliyan 3.4 da ke aiki a ƙasar – ita ce ta shida a jerin ƙasasheb masu arziƙin mai kuma tana cikin manyan ƙawayen Amurka.