Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alhinin mutuwar fitaccen ɗan wasan kwaikwayo Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da ‘Samanja Mazan Fama’.
Ya rasu ne a daren Asabar bayan fama da jinya mai tsawo.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce Shugaban ya kwatanta mutuwar da abu mai ciwo, inda ya ce Samanja ya ba da gudummawa a ƙasar ta hanyoyi daban-daban a tsawon rayuwarsa.
Ya ce faɗakarwa da marigayin ya riƙa yi ta hanyar wasannin kwaikwayo, sun koyar da matasan ƙasar da dama abubuwa masu kyau.
Shugaba Tinubu ya buƙaci iyalan Pategi, da al’ummar jihohin Niger da Kwara, da masarautar Pategi, da masana’antar harkar nishaɗi da su ɗauki dangana


