fidelitybank

Mutuwar Mohbad: An gurfanar da mawaki Naira Marley

Date:

‘Yan sanda a jihar Lagos sun gurfanar da tauraron mawakin Najeriyar nan, Azeez Fashola, wanda kuma ake kira da Naira Marley da takwaransa Balogun Eletu, wanda aka fi sani da suna Sam Larry, game da mutuwar mawaki Ilerioluwa Aloba, wato Mohbad.

‘Yan sanda sun gayyaci Naira Marley da Sam Larry inda suka gurfanar da su a kan kotun majistare da ke Yaba ranar Laraba.

Jaridar Vanguard ta ambato cewa kotun ta bai wa ‘yan sanda damar ci gaba da tsare mutanen biyu don gudanar da bincike.

Mohbad ya mutu ne ranar 12 ga watan Satumban 2023 a Lagos inda aka binne shi washe gari. Sai dai, wadanda ake zargin sun musanta hannu.

Mohbad ya bar kungiyar Marlian Records, wadda ke karkashin Naira Marley a kan wata dambarwa da ta kaure bara, sai dai dangantaka tsakanin marigayin da tsohon shugabansa, ta ci gaba da yin tsami har bayan lokacin.

A lokaci guda kuma, rundunar ‘yan sandan Lagos ta ayyana neman Owodunni Ibrahim wanda aka fi sani da Primeboy, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo, saboda gazawarsa ta amsa gayyatar da suka yi masa a kan mutuwar Mohbad.

Wata sanarwar rundunar da wani mai magana da yawun ‘yan sandan Lagos, SP Benjamin Hundeyin ya fitar a ranar Laraba, ta ce sun dauki matakin ne saboda gazawar Primeboy ta amsa goron gayyatar da aka aika masa tun bayan fara bincike cikin wannan lamari da ya kai ga mutuwar Mohbad.

the nation news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp