Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya jajanta wa fitaccen mawakin nan David Adeleke wanda aka fi sani da Davido da Chioma Rowland bisa rasuwar dan su Ifeanyi.
Osinbajo ya yi addu’a tare da ganin sun rungumi kaddara.
Ya bayyana mutuwar Ifeanyi a matsayin babban rashi.
Osinabjo, a cikin wani sakon Twitter da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Laolu Akande, ya fitar, ya ce, “Mataimakin Shugaban kan mutuwar Ifeanyi: “Dolly & Ni na yi matukar bakin ciki da mummunan rashi na Ifeanyi, masoyi dan Davido & Chioma. Muna addu’a Ubangijinmu Yesu Kristi ya ta’azantar da su kuma ya goyi bayan su duka ta wurin wannan abin takaici. Amin.
“Muna kuma jajantawa dan uwanmu, Dokta Deji Adeleke da daukacin dangin Adeleke. Kullum kuna cikin tunaninmu da addu’o’inmu.”