Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta tsare biyu daga cikin ma’aikata takwas na mawaki David Adeleke wanda aka fi sani da Davido, wadanda aka gayyata domin amsa tambayoyi kan mutuwar dansa mai shekaru uku, Ifeanyi Adeleke.
Ma’aikatan gidan biyu da aka tsare kuma suna dafa abinci yayin da ‘yan sanda suka fara shirin tantance mutanen.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce an tsare mai dafa abinci da nanny, wanda aikinsu shi ne kula da jin dadin yaron, bayan an yi musu tambayoyi sosai.
An bayar da rahoton cewa Ifeanyi ya nutse a cikin wani tafki a gidan mawakin na Banana Island ranar Litinin.
An ruwaito cewa ma’aikaciyar nanny tana tare da yaron lokacin da mai dafa abinci ya zo tare da su. Nanny aka ce ta tashi taji ana waya, ta barshi da mai girki, shima yace ya bar yaron dan shekara uku da nanny.
Daga baya wani jami’in tsaro ya hango Ifeanyi a cikin tafkin bayan mintuna 20.
Marigayin dan daya tilo ne ga Davido tare da mahaifiyarsa na uku, Chioma Rowland.