fidelitybank

Mutun ɗaya ya mutu yayin da kwale-kwale ya kutse da mutane sittin a Sokoto

Date:

Mutum guda ya mutu yayin da fiye da 30 suka nutse bayan wani kwale-kwale ɗauke da mutane ya kife a kogin Dundaye a ƙaramar hukumar Wamakko da ke jihar Sokoto.

Lamarin ya faru ne ranar Lahadi da safe, lokacin da mutanen suka shiga kwale-kwalen domin zuwa gonakinsu.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA mai lura da jahohin Sokoto da Kebbi da Zamfara, Aliyu Shehu-Kafindangiya, ya tabbatar wa da BBC aukuwar lamarin, inda ya ce, jami’an hukumar da gwanayen ninƙaya a ruwa na ƙoƙarin ceto sauran fasinjojin da ba a gani ba.

”Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 10:00 na safe, kuma mun zo da jami’anmu da kuma gwanayen nutso a ruwa domin a san yadda za a ceto waɗannan mutanen da ke cikin ruwa, yanzu dai an fiddo gawa guda kuma an wuce da shi gida domin a yi masa sutura kamar yadda addini ya tanada”, in ji jami’in hukumar NEMA, Aliyu Shehu-Kafindangi.

Matuƙin kwale-kwale wanda shi kaɗai ne da ya tsira, ya shaida wa BBC cewa suna kan hanyarsu ne daga garin na Dundaye zuwa fadama domin aikin shinkafa lokacin da lamarin ya faru.

Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji aƙalla 20 ya kife a jihar Jigawa, lamarin da ya janyo mutuwar aƙalla mutum 15.

Hatsarin kwale-kwale a Najeriya, wani abu ne da ke neman zama babban bala’i, wanda masana ke dangantawa da rashin ingancin jiragen da kuma ƙazamin lodi da ake yi wa kwale-kwalen.

sunnnewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp