fidelitybank

Mutumin da ya siyar da rayuwarsa don kare mutane daga gobarar Tankar Mai

Date:

An yi ta kwarzanta wani mutum, saboda sayar da rayuwarsa da ya yi ya tuƙa wata tankar fetur da ta kama da wuta a ƙoƙarinsa na fitar da ita daga wajen da mutane suke don kar a yi ɓarna a birnin Warri na jihar Delta.

Ejiro Otarigho ya shai da wa BBC cewa “Abu ɗaya ne ya zo raina shi ne in tuƙa tankar mai cin wuta har zuwa wajen kogi mafi kusa.

“Mataimakina ne ya ankarar da ni cewa tankar tamu ta kama da wuta. Kuma wuta ce ganga-ganga ta kama,” a cewarsa.

Mista Ejiro ya sauke wani lodi kenan daga tankar tasa sannan ya kama hanyar zuwa wani wajen sai abin ya faru.

Ba tare da ɓata lokaci ba, ya shaida wa mataimakin nasa ya sauka daga motar inda shi kuma ya ƙara mata wuta don ficewa daga cikin mutane don gudun jawo ɓarna.

A wannan yanayin, duk wani dan kukure daga Mista Otarigho ko kuma a sau wata fashewa, da za su iya jawo mummunan bala’i. In ji BBC.

“Niyyata ita ce na tuƙa motar har zuwa wajen kogi. Amma da na isa can sai sitiyarin motar ya cije sai na kasa ci gaba da tuƙawa,” ya faɗa.

“Na ce idan na tuƙa kai tsaye, motar na iya faɗuwa kuma za ta iya ƙara jawo matsala. Don haka dole na tsaya a wani buɗaɗɗen waje.”

A ƙarshe Mr Otarighoya samu nasarar kawar da tankar daga cikin mutane, kuma a wani bidiyo da ya yaɗu an ga yadda muatne suka baibaye shi suna murna.

Mr Otarigho ya tsira lafiya ba abin da ya same shi sai hayaƙi da ya shaƙa da kuma ƴan raunuka da ji a jikinsa.

www.legit.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Majalisa ta gayyaci Gwamnan Filato kan tsaron jihar

Kwamitin wucin gadi kan matsalolin tsaron jihar Filato na...

Sojoji sun sun kashe ‘yan Boko Haram 24

Rundunar Sojoji ƙarƙashin rundunar 'Operation Hadin Kai' mai yaƙi...

Dangote zai gina rumbum man fetur da dizel a Namibia

Matatar mai ta Dangote da ke Najeriya za ta...

Dangote ya rage farashin litar mai zuwa ₦820

Kamfanin matatar man Dangote ya rage farashin litar mai...

Dubai ta sake tsaurara matakan bai wa ‘yan Najeriya biza

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, UAE ta sake sanya wasu dokoki...

‘Yan Bindigar Katsina ‘yan asalin jihar mu ne – Gwamna

Gwamnan Katsina Umaru Dikko Radda ya ce galibin 'yan...

Zan yi wa ADC aiki ina cikin jam’iyyar PDP – Sule Lamido

Jigo a babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya...

Buhari da Tinubu kan su a hade ya ke – Garba Shehu

Mai magana da yawun tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari...

Ganduje ya kama aiki a hukumar kula da filayen jirgin sama

Tsohon shugaban jam'iyyar APC mai mulki, Abdullahi Ganduje, ya...

JAMB ta amince da maki 150 mafi ƙanƙanta don samun gurbin karatu a jami’o’i

Hukumar shirya jarrabawar shiga Jami'o'i ta Najeriya (JAMB) ta...

ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara

Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya, ASUU da dakatar yajin...

Masu haɗakar ADC na ɓaɓatu ne saboda rashin gwamnati – Radda

Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda ya yi...
X whatsapp