Attajirin nan ɗan ƙasar Afirka ta Kudu, Johann Rupert ya zarce attajirin nan ɗan Najeriya, Aliko Ɗangote a matsayin wanda ya fi kowa arziƙi a nahiyar Afirka, kamar yadda mujallar Bloomberg Billionaires Index.
Mista Rupert shi ne mai kamfanin Richemont wanda ɗaya ne daga cikin manyan kamfanonin da ke samar da kayan alatu da suka haɗa da shagunan Cartier and Montblack da ke sayar da turaren da agoguna da sauransu.
Yawan kuɗin attajirin sun ƙaru zuwa dala biliyan 14.3 daga dala biliyan 1.9, abin ya sa ya zama mai kuɗin duniya na 147 inda ya bai wa Ɗangote na Najeriya tazarar mutum 12.
Arziƙin Ɗangote dai ya ragu ne da dala biliyan ɗaya da miliyan ɗari bakwai ($1.7bn) a shekarar nan ta 2024, abin da ya mayar da yawan dukiyarsa zuwa dala biliyan 13.4, in ji mujallar Bloomberg.
A yanzu haka shi wannan attajirin ɗan Afirka ta Kudu na zaune ne a birnin Cape Town a wani gidan ƙasaita sannan yana da wasu ƙarin gidajen a biranen Geneva da London.
Nicky Oppenheimer, wanda shi ma ɗan Afirka ta Kudun ne shi ne mutum na uku da ke biyewa Ɗangote a masu kuɗin nahiyar Afirka, inda aka ƙimanta yawan dukiyarsa a kan dala biliyan 11.3.
Sai kuma Nassef Sawiris ɗan ƙasar Masar ne ke biye masa da arziƙi mai yawan dala biliyan 9.48. Sai kuma Natie Kirsh shi ma ɗan Afirka ta Kudu da ya zama na biyar a masu kuɗin Afirka inda yake da arziki mai yawan dalar Amurka biliyan 9.22.
Kamar dai mujallar Forbe, ita ma Bloomberg tana amfani da sauye-sauyen da ake samu a hawa da saukar dukiyar attajirai lokaci zuwa lokaci.
Kambun mutumin da ya fi kowa arziƙi na Afirka ka iya ci gaba da sauyawa a tsakanin attajiran bisa la’akari da yadda kasuwa ke jujjuyawa.