Kafafen watsa labaran Amurka dai sun bayyana Ryan Wesley Routh a matsayin wanda ake zargi sakamakon yunƙurin kisan ɗantakarar shugabancin Amurka na jam’iyyar Republican, Donald Trump, a Florida.
Mista Routh, mai shekara 58 dai ɗan North Carolina ne inda ya shafe fiye da rabin rayuwarsa a can kamar yadda bayanai masu inganci suka nuna, sai dai kuma a baya-bayan nan ya koma Hawaii da zama.
Abin da ya aikata ya sanya ana bincike kansa kuma wani abu da ya fito fili shi ne cewa yana da aƙida sosai ta ƙaunar Ukraine. Sannan ya yi shari’u da dama da jama’a.
Ana dai zargin Ryan da zuwa filin wasan ƙwallon Golf da ke Florida ranar Lahadi, yana ɗauke da bindiga ƙirar AK-47.
Jami’an FBI sun karɓi bindigar da kuma jakunkuna guda biyu na goyawa a baya daga dajin da ake zargin ɗanbindigar ya ɓoye su. In ji BBC.
Duk da cewa Routh ya tsere a motarsa, amma wani wanda ya shaida al’amarin ya gano shi bayan ɗaukar hotonsa a cikin baƙar motarsa ƙirar Nissan.
Daga nan ne aka fitar da hoton motar ana neman ta. Ƴansandan yankin sun ce jami’ansu sun gano motar miniti 45 bayan faruwar al’amarin kuma suka bi ta.
Kuma daga ƙarshe an tsayar da shi a kan babban titin Interstate 95 inda aka tafi da shi domin tsarewa.