fidelitybank

Mutum uku sun rasu a hanyar Bauchi zuwa Kano

Date:

Da sanyin safiyar ranar Litinin ne wasu maza biyu da yarinya mace daya suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota daya tilo da ya afku a kauyen Gada Data dake kan hanyar Bauchi zuwa Kano a karamar hukumar Ganjuwa a jihar Bauchi.

Wasu fasinjoji tara na wata motar bas ta Hummer dauke da fasinjoji 22 sun samu raunuka daban-daban a hadarin, wanda aka ce ya faru ne da misalin karfe 12:13 na safe.

Rahoton da hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi ta fitar ta bayyana cewa, motar bus din kasuwanci na dauke da lamba: GKA519 XA.

Karanta Wannan: Mutane 15 sun mutu a hanyar Kogi – FRSC

Rahoton ya nuna cewa an kai rahoton afkuwar hatsarin ga jami’an hukumar bayan mintuna 10 da faruwar lamarin, inda nan take aka tura jami’an kiyaye haddura zuwa wurin domin gudanar da aikin ceto.

Ya kara da cewa jami’an sun garzaya da wadanda lamarin ya rutsa da su: manya maza biyar, manya mata uku, yara maza biyu da yara mata zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) da ke Bauchi, inda likita ya tabbatar da rasuwar marigayin.

Wadanda suka jikkata a cewar rahoton sun hada da manya maza uku, manyan mata uku, yara maza biyu da mace daya.

Daga nan ya bayyana cewa an ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa na ATBUTH, inda kuma za a mika su ga ‘yan uwansu domin yi musu jana’iza.

legit breaking news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp