Gwamnatin jihar Ogun, ta tabbatar da samun sabbin masu dauke da cutar ƙyandar Biri guda hudu, wanda ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar a jihar zuwa bakwai.
Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Tomi Coker ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da kwamishinan lafiya na jihar Abeokuta ya rabawa manema labarai.
Sanarwar ta ce, an gano wasu guda biyu a Ota, a cikin karamar hukumar Ado-Odo/Ota, yayin da Abeokuta ta Arewa da Abeokuta ta Kudu ke da guda daya.
Sanarwar ta bayyana cewa Jami’an Sa-ido da Sanarwa da Cututtuka (DSNOs) a kananan hukumomin da abin ya shafa sun gudanar da jerin layukan da suka shafi tuntubar juna, inda ta nuna cewa tuni majinyatan sun sha magungunan da aka rubuta.
Sannan kuma ta shawarci mazauna yankin da su guji cudanya kai tsaye da ruwan jiki ko ciwon masu rai ko matattun dabbobi, mutane ko gurbatattun abubuwa, kamar yadda ta jaddada wanke hannu da sabulu da ruwa akai-akai, musamman bayan ziyara ko kula da mara lafiya.
Yayin da ya kara da cewa ya kamata a dafa abincin dabbobi yadda ya kamata kafin a ci abinci, gwamnati ta yi kira da a kwantar da hankula daga mazauna yankin, tare da tabbatar da daukar matakan da suka dace don dakile yaduwar cutar.


