fidelitybank

Mutum hudu sun mutu a wani rikicin fili a jihar Ebonyi

Date:

Mutum huɗu sun mutu sakamakon rikici game da wani fili tsakanin garuruwa biyu na jihar Ebonyi da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa rikicin ya ɓarke ne tsakanin mazauna ƙauyukan Ogwor da Umuobor saboda wani yanki da ake kira Elueke.

Rahoton ya ce gwamnatin jihar ta ayyana yankin a matsayin “ba na kowa ba” a farkon watan Janairu, kuma ta umarci duka ƙauyukan su ƙaurace wa yankin.

“Daga cikin mutum huɗu da aka kashe, an ce uku sun je nome doya ne a yankin ranar Laraba, kafin a kashe wata mace a ranar Litinin,” a cewar Chinasa Okorie, shugaban cibiyar Akaeze Development.

Sai dai kakakin rundunar ‘yansanda a jihar, Joshua Ukandu, ya ce kisan wata mace kawai suka sani a ranar Litinin da ta gabata, amma ya ce suna ci gaba da bincika lamarin.

breaking news in nigeria today punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp