fidelitybank

Mutum Hudu sun mutu, 15 sun fada komar ‘yan sanda yayin arangama a Kogi

Date:

Rikicin da ya sake barkewa tsakanin wasu kungiyoyin asiri biyu ya yi sanadin mutuwar mutane hudu, yayin da aka kone gidaje kusan biyar a yankin Kabawa da ke karamar hukumar Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

Jaridar THISDAY ta samu tabbataccen cewa, rikicin ya samo asali ne a daren ranar Litinin din da ta gabata a lokacin da kungiyoyin biyu masu gaba da juna da mambobi ‘yan kasa da shekaru 13,14, da kuma shekaru 15 suka tsunduma kansu cikin neman ‘yanci, wanda ya yi sanadin kashe-kashe da kona gidaje a Kabawa, wani yanki na asali.

Rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa ya sa mazauna yankin sun kwashe iyalansu daga yankin zuwa wani wuri, domin yin hijirar dole, saboda gujewa fadawa cikin rikicin.

Majiyoyin cikin gida sun yi nuni da cewa, rikicin ya samo asali ne sakamakon ramuwar gayya da wata kungiya ta yi bayan kashe daya daga cikin mambobinsu.

Majiyar ta kara da cewa ‘yan ta’addan wadanda ke dauke da bindigu da wasu muggan makamai sun mamaye wasu gidaje, inda suka far wa mutane tare da kona gidajen da suke kyautata zaton ‘yan kungiyar ne.

Sai dai yayin da ‘yan sanda suka mamaye yankin a jiya, domin kwantar da hankulan, wasu daga cikin ‘yan kungiyar asiri sun yi ta artabu da jami’an tsaro, wanda ya dauki tsawon sa’o’i da dama kafin daga bisani a samu nasara. An tattaro cewa wasu daga cikin ‘yan kungiyar asiri sun tsallake rijiya da baya a cikin kogin Nijar, domin gudun kada ‘yan sanda su kama su, suka tsallaka zuwa wancan gefen kogin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, SP William Aya, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce, rundunar ta kama mutane 15 da ake zargi.

Aya ya bayyana cewa, rundunar ta tabbatar da cew, an kashe mutum daya ne kawai
ana ci gaba da binciken abin da ya kai ga faruwar lamarin.

 

daily post nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp