Mutum fiye da 67,000 ne suka tsallaka Sudan ta Kudu tun bayan fara rikici a maƙwabciyarta Sudan a watan Afrilu.
Ya zuwa safiyar yau Lahadi, Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar da shigar mutum 67, 087 cikin ƙasar ta garuruwa 13 na kan iyakar ƙasashen biyu.
Akasarinsu ‘yan asalin Sudan ta Kudu ne da suka tsere wa yaƙin da ƙasarsu ta shafe shekaru tana fama tskaanin shugabanninta.
Ƙasar da ke cikin ƙasashen duniya mafiya talauci, Sudan ta Kudu na fuskantar ƙalubalen kula da sabbin mutanen da kuma mayar da su gidajensu.
Rikicin Sudan tsakanin Janar Burhan da dakarun rundunar RSF ƙarƙashin jagorancin Janar Daghalo ya jawo kisan ɗaruruwan mutane tare da raba wasu fiye da miliyan ɗaya da muhallansu.