Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, ta tabbatar da mutuwar mutum guda tare da bayyana batan wani mutum a wani hari da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai a karamar hukumar Isin a ranar Talata.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Okasanmi Ajayi, ya tabbatar da faruwar lamarin a Ilorin ranar Laraba.
Ko da yake rahotanni sun ce an yi garkuwa da mutane da dama a lamarin, amma kakakin ya ce mutum daya ne ya bata.
“An kashe mutum daya, daya kuma ba a ganta ba bisa ga bayanin da ake samu,” in ji shi.
Ya ce an tura ‘yan sanda zuwa wurin a ranar Talata.
“Zan fitar da cikakkun bayanai da zarar an samu don Allah,” Okasanmi ya kara da cewa.
Rahotanni na cewa, an yi garkuwa da mutanen ne a ranar Talata a tsakanin titin Ijara/Isanlu a karamar hukumar.
An shiga fargaba a yankin yayin da rahotanni suka ce wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da mutane da dama tare da kashe wani mutum daya kawai mai suna Mista Adeyemi wanda ya fito daga Pamọ Isin.