fidelitybank

Mutum daya ya mutu a cikin mutane hamsin da suka nutse a cikin Kogin Neja

Date:

An samu rahoton mutuwar mutum daya, yayin da wani kuma ya samu raunuka, bayan da wani kwale-kwalen da ke dauke da ‘yan kasuwa 50 daga Shiroro zuwa Kasuwar Kwata da ke Zumba a karamar hukumar Shiroro ta Jihar Neja ya kife a tsakiyar kogin Zumba.

Aminiya ta tattaro cewa, mutum shida ne kawai aka ceto daga cikin fasinjojin, kuma an tabbatar da mutuwar mutum daya.

An bayyana cewa hatsarin ya afku ne da yammacin ranar Asabar.

Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Ibrahim Inga, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin, sai dai ya ce bai samu cikakken bayani kan asarar rayuka ba.

Sarkin Ruwa, Kwata-Zumba, Umar Isah, ya shaida cewa, injin kwale-kwalen da ke jigilar ‘yan kasuwar da suka hada da mata, yara, shanu, awaki da dama, kwandunan kifi da amfanin gona ya ruguje a tsakiyar kogin. .

Ya tabbatar da cewa ,daya daga cikin fasinjojin ya rasa ransa yayin da aka ceto wasu 6 da ransu, inda ya ce an yi asarar shanu 3 da awaki da sauran kayayyaki.

legit ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...
X whatsapp