Akalla mutane biyu a Sri Lanka sun mutu a lokacin da suke jiran dogayen layukan neman mai, yayin da karancin abinci ya haifar da zullumi da wahala a fadin kasar.
Kasar Sri Lanka na fama da matsalar tattalin arziki mafi muni a tarihinta a matsayinta na kasa mai cin gashin kanta, tare da rashin samun kudaden waje, domin siyan muhimman kayayyaki da ake shigowa da su kasar yana raguwar samar da muhimman kayayyaki.
A na tilastawa masu ababen hawa su jira sa’o’i a wajen gidajen mai, domin samun mai sannan gwamnati ta sanya dokar hana fita, saboda kamfanonin wutar lantarki ba su iya biyan isassun man fetur daga kasashen waje domin biyan bukata.
‘Yan sanda sun ce, wani dattijo mai shekaru 70 da ke kan layi domin siyan mai ya fadi kuma ya mutu a wani gidan mai da ke wajen babban birnin kasar Colombo ranar Lahadi.
Wannan dai shi ne karo na biyu da irin wannan mutuwa a cikin kwanaki da dama, bayan da wani dattijo ya fadi a garin Kandy a lokacin da yake jiran man kananzir ya yi amfani da shi, kamar yadda ‘yan sanda a birnin suka tabbatar.
Kafofin yada labaran cikin gida sun ce, wasu mata da dama da ke tsaye a cikin rana mai zafi domiin sayen gas sun suma a wurare da dama a tsibirin a karshen mako.
Masu jigilar man fetur da iskar gas sun yi zaman dirshan a babban tashar jiragen ruwa na Colombo, inda masu shigo da kaya suka kasa zayyano isassun kudaden kasashen waje domin biyan su.
Barkewar cutar ta Covid-19 ta durkusar da bangaren yawon shakatawa na Sri Lanka – babban mai samun kudin waje – kuma kudaden da ma’aikatan kasashen waje ke aikawa su ma sun ragu.
Hukumomin kasar sun sanar a makon da ya gabata cewa kasar za ta nemi tallafin IMF, don magance matsalar basussukan kasashen waje da ke kara tabarbarewa da kuma tara kudaden ajiyarta.
Hukumomin kididdigewa da masu sharhi na kasashen waje sun nuna shakku kan ikon da kasar da ke da karancin kudi na iya biyan bashin da ta ke bi na dala biliyan 51 a waje, tare da biyan dala biliyan 6.9 a bana.
Karancin ya yi barna a kusan kowane fanni na rayuwar yau da kullum, inda a wannan makon hukumomi suka dage jarabawar wa’adin dalibai kusan miliyan uku.
Kamfanin samar da wutar lantarki na tsibirin ya kuma ce, ba ya da takarda don buga takardun kudi na wata-wata ga miliyoyin masu amfani da su.