fidelitybank

Mutum biyu sun rasa ransu bayan kifewar kwale-kwale a Rimin Gado

Date:

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane biyu a cikin wani kogi, bayan da kwale-kwalen su ya nutse a Zangon Durgu zuwa kauyen Kanya da ke karamar hukumar Rimin Gado.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na hukumar, SFS Saminu Yusif, ya ce, an ceto biyu da ransu, yayin da wasu biyu kuma suka rasa rayukansu nan take.

Ya ce, jami’an kashe gobara sun dauki matakin gaggawa ne, bayan da suka samu kira daga wani Barista Munir Dahiru, wanda ya kai musu rahoton faruwar lamarin da karfe 12:30 na ranar Litinin.

Ya kuma ce, mutane hudu ne lamarin ya rutsa da su, wanda suka ceto biyu sai dai kuma Sani Shitu mai shekaru 25 da Jabir Sabiu mai shekaru 30 sun rasa ransu a cikin ruwan.

Wadanda aka ceto sun hada da Sha’aban Bala mai shekaru 35 da Rabiu Bashari mai shekaru 30 a duniya, wanda suka mika su ga mataimakin shugaban karamar hukumar Rimin Gado, Shafi’u Abdullahi Gulu domin tattaunawa da alakar su domin daukar mataki na gaba.

Yusif ya kuma shawarci daukacin mutanen da ke amfani da kwale-kwale da su yi taka tsan-tsan ta hanyar yin amfani da jirgin ruwan a yankunan su.

legit nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp